Ranieri ya ce Mourinho koci ne da ya san aikinsa

Claudio Ranieri ya ce Mourinho gwarzo ne

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Leicester, Claudio Ranieri, ya ce kocin Manchester United Jose Mourinho "mutum ne da ya san aikinsa" kuma duk rashin jituwar da ta faru a tsakaninsu a baya "ta wuce".

Leicester za ta fafata da United a Old Trafford ranar Asabar, ko da yake kociyoyin biyu sun sha yin fama da rashin jituwa a baya.

Mourinho ya bayyana Ranieri da cewa "ya gaza" bayan ya maye gurbinsa a matsayin kocin Chelsea sannan ya taba cin mutumcinsa a lokacin yana kocin Inter Milan.

Ranieri ya ce: "Mourinho koci ne da ya san aikinsa, wanda ke da kwazo da wayo. Rashin jituwar da ta auku a tsakanimu a baya ta zama tarihi."

Mourinho ne ya maye gurbin Ranieri a Chelsea a shekarar 2004 kuma ya ce kulob din yana ganin dan kasar ta Italiya a matsayin "wanda ya gaza."