Masana sun gano yadda dawakai ke 'magana' da mutane

Dawakan na yin ishara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An gudanar da bincike kan dawakai da yawa

Masana kimiyya a kasar Norway sun gano cewa dawakai suna iya yin sadarwa tsakaninsu da mutane ta hanyar ishara.

Masanan sun bai wa wani rukunin dawakai horo kan yadda za su taɓa alamomi daban-daban a wani allo domin nuna cewa suna so a yi musu wani abu, misali idan suna so a lulluɓe su da bargo sakamakon jin sanyi.

Sakamakon ya nuna cewa zabin da suke yi ya danganta ne da irin yanayin da ake ciki -- na sanyi ko zafi.

Haka kuma sakamakon ya nuna cewa suna yin zabin ne domin radin kansu, abin da ke nuna cewa lallai sun san abin da suke yi.