Kotun ta kawo karshen ce-ce-ku-ce kan zaben Gabon

Mutanen yankinsa dai sun yi zabe dari bisa dari

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto,

Ali Bongo ya gaji mahaifinsa Omar Bongo wanda ya jagoranci Gabon daga 1967 har mutuwarsa a 2009

A hukuncin da ta yanke na yanzu kotun kolin ta ce Ali Bongo ya samu kashi 50.66 cikin dari fiye da sakamakon farko, yayin da bokin hamayyyarsa Jean Ping ya samu kashi 47.24 cikin dari.

Ali Bongo ya samu sakamakon da ya zarta na farko da aka sanar ne saboda kotun ba ta soke kuri'un yankin da shugaban ya fi karfi ba na Haut-Ogoue.

Sai dai kuma kotun ta soke kuri'un mazabu 21 a Libreville kamar yadda kwamitin yakin neman zaben shugaban ya bukata.

Sakamakon farko dai na zaben wanda aka gudanar ranar 27 ga watan Agusta ya nuna cewa shugaba mai ci, Ali Bongo ne ya ci da kuri'a kasa da dubu shida tsakaninsa da Mista Ping.

Wannan ne kuma ya haifar da tashin hankali lamrin da har yanzu ya sa ake zaman dar-dar yayin jiran hukuncin kotun kolin, har ta kai mutane na ta sayen kayan abinci suna tarawa a gida don gudun abin da zai iya faruwa.

Masu hamayya a rubuce-rubucen da suka yi sun bukaci kotu ta sake kirga kuri'un da aka kada a mahaifar shugaban kasar da ke yamamcin kasar, inda aka ce mutane sun fito zaben kusan dari bisa dari.