Obama ya hana a kai Saudiyya kotu

Saudiyya dai ta sha musanta kai harin 11 ga Satumba

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Shugaban Amurka, Barack Obama ba ya son a kai Saudiyya kara

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya ki yarda iyalai da 'yan uwan mutanen da suka mutu a harin ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba, su kai Saudiyya a kotu.

A farkon wannan watan ne dai 'yan majalisar dokokin Amurka suka amince da kudirin dokar da ya ba wa iyalan matatan damar jefa Saudiyya a kotu.

Mista Obama ya ce idan aka bari mutanen suka maka Saudiyya a kotu, to hakan zai lalata burace-buracen da kasar ta Amurka take da su.

An dai ce mafiya yawancin mutanen da suka karkatar da akalar jiragen da suka kai hari a ranar 11 ga watan na Satumba, 'yan kasar Saudiyya ne.

Sai dai kuma hukumomi a Saudiyya sun sha musanta hakan.