Snapchat ya kaddamar da tabarau mai na'urar daukar hoto

Snapchat ya kaddamar da tabarau mai kyamara

Asalin hoton, SNAP

Bayanan hoto,

Tabaran zai iya nadar hoton bidiyo na tsawon dakika 30 a lokaci guda

Kamfanin sada zumunta da aikewa da sako na Snapchat ya kaddamar da tabarau wanda ke da na'urar daukar hoto.

Snapchat ya ce zai fara sayar da tabaran nan gaba a wannan shekarar a kan $130.

Tabaran zai iya nadar hoton bidiyo na tsawon dakika 30 a lokaci guda, in ji kamfanin.

Kamfanin ya kuma sauya sunansa daga Snapchat zuwa Snap, Inc.

Ya ce ya dauki matakin ne a yunkurin da yake yi na sauyawa daga kamfanin aikewa da sakonni zuwa wanda zai rika yin abubuwa da dama.