Dan kunar bakin wake ya tayar da bama bamai a Bagadaza

Ana yawan kai hare-hare a Bagadaza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane da dama sun jikkata

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bama baman da ke jikinsa a birnin Bagadaza na kasar Iraki, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum shida.

Mutumin ya tayar da bama baman ne a lardin Iskan inda 'yan Shi'a suka fi zama.

Har yanzu dai ba a san kungiyar da ta bayar da umarnin tayar da bama baman ba.

Sai dai kungiyar IS mai ikirarin kishin Musulinci ta sha kai hare-hare a birnin na Bagadaza da kewaye.