An kashe marubucin da ake zargi da yin 'ridda' a Jordan

Hattar ya musanta zargin
Bayanan hoto,

Ana zargin Hattar da zagin Allah

An kashe marubucin nan dan kasar Jordan wanda ake zargi da yin ridda.

A watan jiya ne dai aka kama Nahid Hattar saboda ya yi wasu zane-zane da ke yin isgili ga addinin Musulinci, inda ake sa ran za a fara yi masa shari'a ranar Lahadi.

Sai dai ya ce bai yi zane-zanen da nufin cin mutuncin addinin Musulinci ba.

Kamfanin dillancin labaran kasar, Petra, ya rawaito cewa an harbi Hattar sau uku a wajen kotun da za ta yi masa shari'a a birnin Amman.

Hukumomi dai sun ce ya keta dokokin kasar saboda wallafa zane-zanen da ya yi.