Ni ne shugaban kasar Gabon — Jean Ping

Jean Ping ya ce shi ne ya ci zabe saboda haka ba zai lamunce da hukuncin Kotun Tsarin Mulki ba
Bayanan hoto,

Abokin hamayyar Ali Bongo, Jean Ping

Abokin takarar Ali Bongo na shugabancin kasar Gabon, Jean Ping, ya ce shi ne shugaban kasa.

Jean Ping dai ya shaida hakan ga magoya bayansa a ranar Asabar, bayan Kotun Tsarin Mulkin kasar ta tabbatar da nasara ga shugaba mai ci, Ali Bongo.

Wani mazaunin birnin Livrabille, ya shaida wa BBC cewa shugaban adawar, ya nemi magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu.

Ya kuma ce ce ba zai hakura da bayyana shi da kotun ta yi a matsayin wanda ya sha kaye ba.

Kotun kolin dai ta ce Ali Bongo ya samu kashi 50.66 na kuri'un da aka kada, yayin da abokin hamayyyarsa, Jean Ping, ya samu kashi 47.24.

Ali Bongo ya samu sakamakon da ya zarta na farko da aka sanar ne saboda kotun ba ta soke kuri'un yankin da shugaban ya fi karfi ba na Haut-Ogoue.

A ranar Juma'a dai, kafin sanar da sakamakon, al'ummar kasar sun yi wa kasuwanni tsinke domin sayen kayan masarufi saboda fargabar sake barkewar wani sabon rikicin.