An fatattaki 'yan luwadi a Uganda

An dai so a yi dokar da za ta haramta luwadi a Uganda
Bayanan hoto,

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Musevni

'Yan sanda sun fatattaki masu luwadi daga wuraren da suke sheke aya.

An dai ce 'yan luwadin suna shagalin bikin aure ne a wasu wurare guda biya da ke kusa da tafkin Lake Victoria, a Kampala.

Daman dai ministan samar da Da'a da kare mutunci na kasar, ya sha alwashin daukar tsauraran matakai kan shagulgulan na masu luwadi.

A shekarar 2014 ne dai aka soke batun yin dokar da za ta ba sanya yin luwadi a jerin aikata manyan laifuka, a Uganda.