Sojojin Najeriya sun ce idan Shekau ba a raunata shi ba to ya mike tsaye

Sojojin Najeriya sun sha cewa sun raunata Abubakar Shekau
Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani kan wani faifan bidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar, a inda ya karyata sojojin kan cewa sun raunata shi.
Da sanyin safiyar ranar Lahadi ne dai kungiyar ta saki faifan bidiyon a shafin intanet.
A cikin bidiyon, Abubakar Shekau ya kwashe kimanin minti 40 yana magana da harsunan Hausa da Larabaci da Turanci da kuma Kanuri.
Da fari dai ya karyata rundunar sojin Najeriya da ta bayar da sanarwar raunata shi a wani harin sama da ta ce ta kai kan 'yan Boko Haram.
Shekau ya ce yana nan lafiya kalau babu abin da ya same shi.
Hakan ne ya sa rundunar sojin ta Najeriya, ta mayar da martani, a inda ta bayyana kalaman Shekau da rashin hankali.
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai ya lashi takobin kakkabe 'yan Boko Haram daga Najeriya.
Mai magana da yawun rundunar, Kanar Sani Kukasheka Usman ya shaida wa BBC cewa hakika sojojin sun raunata shi a lokacin hare-haren.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Kanar Usman ya ce idan har Shekau ya ce ba a raunata shi ba, to mai yasa bai mike tsaye ba a bidiyon.
Ya kuma kara da cewa duk abubuwan da Abubakar Shekau yake yi alamu ne da ke nuna cewa ruwa ya kusa kare wa dan kada.
Dangane kuma da ikrarin da sojojin Najeriyar suka sha yi na cewa sun kashe Shekau, Kanar Usman ya ce gwamnatin baya ce ta yi wannan batu.
Shi dai Abubakar Shekau, baya ga karyata sojojin Najeriya da ya yi, ya kuma bayyana Najeriya da kasar kafirci.
Ya kuma rera taken Najeriya da Turanci, bayan ya bayyana shi da wata alama ta kafirci.
Abubakar Shekau ya kara da shan alwashin ci gaba da kai hare-hare a Najeriya, har zuwa lokacin da kasar za ta koma kan tafarki irin nasu.
Har wa yau, Shekau ya ja hankalin mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya da kuma jagoransu, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da cewa su tuba domin abin da suke yi ba Musulunci ba ne.
Ya kuma kara da cewa tafarkin da 'yan Boko Haram suke bi ne kawai mafita ga mabiya mazhabar ta Shi'a.
Sharhi
Sojojin Najeriya sun sha ikrarin kashe Abubakar Shekau, a yayin wasu hare-haren da suke kai wa Dajin Sabisa.
Kuma a duk lokacin da suka yi irin wannan ikrarin, Shekau din da kansa yake fitowa ya karyata batun nasu.
Ikrarin sojojin kan illata Shekau na baya-bayan nan shi ne wanda sojojin kasar suka ce wani hari da dakarun sama suka kai ya kashe wasu jiga-jigai a ƙungiyar Boko Haram.
Wata sanarwa da kakakin sojan ƙasa, Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar, ta ce an jikkata daya daga cikin shugabannin Boko Haram, wato Abubakar Shekau.
Daga cikin manyan 'yan kungiyar ta Boko Haram da aka kashe yayin harin sun haɗa da Abubakar Mubi, da Malam Nuhu da Malam Hamman.
Sanarwar ta kuma ce, an kai harin ne a ƙauyen Taye da ke yankin Gombale a dajin Sambisa.
Hare-haren Boko Haram kan Shi'a
Tun watan Disamban 2015 El-Zakzaky yake tsare a hannun jami'an tsaro
Kungiyar ta Boko Haram dai, a sakonni bidiyon da ta dade tana fitarwa, ta sha sukar mabiya mazhabar Shi'a.
Ta kuma sha alwashin kaddamar da hare-hare a kan mabiya mazhabar, baya ga kiran jagoran kungiyar ta Shi'a, El-zakzaky da ya tuba.
A baya dai an taba kai wa 'yan Shi'ar harin kunar-bakin-wake a yayin wani tattaki da suke yi daga birnin Kano zuwa Zaria, a arewacin Najeriya.
Jim kadan bayan faruwar al'amarin, kungiyar ta Boko Haram ta dauki alhakin kai harin a kan 'yan Shi'a, a inda ta bayyana su da wadanda ba Musulmai ba.
Boko Haram dai tana ikrarin ginuwa a kan akidun Ahlussunnah da sahabbai suka bi, a inda su kuma 'yan Shi'a suke cewa suna bin mazhabar Iyalan gidan annabi ne.
Ko a kasashe kamar Iraq da Syria da Yemen da ma Saudiyya, ana samun yanayin da kungiyar IS wadda Boko Haram ta yi wa Mubaya'a, ke halasta jinin 'yan Shi'a.
Boko Haram ta dare gida biyu
Yanzu haka za a iya cewa kan 'yan kungiyar Boko Haram ya rabu gida biyu, tsakanin tsagin Abubakar Shekau da na Albarnawi wanda aka ce dan tsohon shugaban kungiyar ne, marigayi Muhammad Yusuf.
Ana zaton cewa rarrabuwar kan dai ta samo asali ne daga kallon da bangaren Albarnawi suke yi wa bangaren Shekau da zarmewa wajen zafafa hare-hare a kan mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Yanzu haka dai Albarnawi ne shugaban kungiyar ta Boko Haram da kungiyar IS ta san da zamansa a Najeriya.