Marubucin Alkur'ani a Najeriya Sharu Bala ya rasu

Writer
Bayanan hoto,

Gwani Mahiru Sharu Bala

A Najeriya, shahararren marubucin Alkur'anin nan bugun Warshu, Mahiru Sharu Bala Gabari ya rasu.

Shi ne ya rubuta Alkur'anin da aka fi amfani da shi a kasar Hausa bugun hannu, kuma yake ci gaba buga shi da yada shi.

Sharu Bala mahaddacin Alkur'ani ne, wanda ya kai matsayi mafi girma a wajen haddar Alkur'ani, har ma ya samu taken Mahiru.

Ya samar da sauye-sauye da dama wajen yadda ake rubuta Alkur'ani a kasar Hausa, kamar banbanta nau'in wasu alamu ko wasula a Alkur'ani bugun dutse.

Baya ga masana'atar buga Alkur'ani da sauran litattafai da yake da ita a Nigeria, ana kuma buga masa Alkur'anai a kasashen waje, kamar Masar.

A baya-bayannan ya kai Alkur'anin da ya rubuta jami'an Azahar ta Masar domin tantance ingancin rubutun, wanda hakan zai sa ya samu karin karbuwa a fadin duniya.

Ya rasu yana da kimanin shekara 88, kuma kafin rasuwarsa, Mahiru Sharu Bala jagora ne a darikar Kadiriyya.

Marigayin ya rasu ya bar 'ya'ya da dama.