Za a ci tarar Yingluck Shinawatra kan tallafin shinkafa

Tsohuwar Firayiminista
Bayanan hoto,

Yingluck Shinawatra

Gwamnatin soji ta kasar Thailand ta na neman cin tarar tsohuwar Firayiministar kasar, Yingluck Shinawatra, saboda shirin tallafi na biliyoyin daloli ga manoman shinkafa da ta bullo da shi lokacin da ta ke ofis.

Shirin ya ba manoman shinkafa damar sayar da amfanin gonakinsu a farashi mai tsada.

Wani kwamiti da gwamnatin ta kafa ya ce tsohuwar Firayiministar ta aikata babban laifi na sakaci, da ta bullo da shirin da bai da riba.

A shekarar 2013 ne aka zabi Yingluck Shinawatra, amma aka hambarar da ita a wani juyin mulki shekaru biyu da suka gabata.

Ta ce sojojin da suka shirya juyin mulkin na bin ta da sharri yanzu.