Ba zan bayyana a gaban kwamiti ba — Jibril

Shugaban Majalisar Yakubu Dogara ya ce shi bai san ma wani abu cushe ba.

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Abdulmumin Jibril ya zargi shugaban Majalisar Wakilan da wasu shugabanninta da cushen makudan kudade a kasafin kudin 2016

Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudin Majalisar Wakilan Najeriya, Hon, Abdulmumini Jibrin, ya ce ba zai bayyana a gaban Kwamitin Da'a na majalisar ba, ranar Litinin.

A makon jiya ne dai majalisar ta umarci kwamitin da ya binciki Hon. Abdulmumini Jibrin kan zargin yin kalaman bata suna ga majalisar.

Jibril ya fasa kwai kan cushen makudan kudaden da zauren ya yi, a kasafin kudin kasar na 2016.

Kwamitin dai ya gayyaci dan majalisar da ya bayyana gabansa ranar Litinin.

To amma a ranar Lahadi ne Abdulmumin Jibril din ya kira wani taron manema labarai, inda ya sanar da cewa ba zai mutunta gayyatar kwamitin ba.

Abdulmumin ya ce ya yanke shawarar kin zuwa ne sakamakon rashin adalci da ya gano ba za a yi masa ba.

Ya ce dalilinsa shi ne mutanen da za su jagorancin kwamitin 'yan amshin shatan shugaban majalisar ne, Yakubu Dogara.