BH: 'Yan gudun hijira na dogaro da kansu

'Yan gudun hijra da dma sukan shiga yanayi na rashin wdatar abinci

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wasu tarin 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram

Wasu 'yan Njeriya da rikicin Boko Haram ya tilasta wa yin hijira zuwa garin Mora na lardin arewa mai nisa a Kamaru, sun soma yin kananan sana'oi domin dogaro da kai.

Wata mata daga cikin 'yan gudun hijirar wadda ta ce ba ta san inda mijinta yake ba kuma 'ya'yanta uku a cikin hudu su ma ba ta san inda suke ba, a yanzu tana yin shayin sayarwa ne domin samun rufin asiri.

Duk da cewa, wani lokaci suna samun tallafin abinci daga hukuma mai kula da 'yan hijra ta majalisar dinkin duniya, amma wasunsu suna ta kokarin su dogara da kansu.

Kimanin shekara biyu kenan tun bayan hare-haren Boko Haram a garin Amchide da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, ya tilasta wa jama'a da dama gudun hijirar zuwa Kamaru.