Cinikin Fetur: Najeriya ta roki Amurka

Gwamnatin Muhammadu Buhari na son ganin Amurka ta dawo sayen danyen man Najeriya
Najeriya ta roki Amurka da ta dage matakin daina sayen danyen man fetur dinta, tana mai cewa matakin bai dace da tsarin bunkasar kasuwanci da mu'amullar tattalin arziki ba.
Ministan kwadago da ayyuka, na Najeriyar, Sanata Chris Ngige, ya yi rokon a birnin Washington na Amurka yayin taron ministoci kan shirin bunkasar Afrika (AGOA) da samar da dama, a ma'aikatar kwadago ta Amurka.
Ngige ya ce daina sayen man da Amurka ta yi, ya sa kudaden da Najeriya ke samu ya ragu kuma hakan ya shafi hatta wasu kasashen Afrika.
Ministan ya ce sauya wannan shawara ta Amurka a kan Najeriy na daya daga matakan da za su taimaka wa Najeriyar ta iya kare 'yanci da hakkin ma'aikata.
Raguwar kudaden wajen na Najeriya kuma ya sa tana kasa aiwatar da wasu ka'idoji na kwadago, kamar hana yara shiga ayyukan kwadago da safarar dan adam da ci da biyan ma'aikata albashi dan kadan.
Dakta Ngige ya bukaci Amurka ta taimaka wa kasashen Afurka tattalin arzikinsu ya bunkasa ta fannin aikin gona, a hanyoyin ilmantar da manoma