Colombia: Yarjejeniyar zaman lafiya za ta gina kasa

Mista Santos ya ce yarjejeniyar za ta kawo karshen fadan ne kawai amma ba wahalar da ake sha ba
Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos ya ce jarjeniyar zaman lafiya da za a kulla tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Farc za ta bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ya shaida wa BBC a wata hira ta musamman cewa "a koda yaushe zaman lafiya ya fi yaki".
A ranar Lintini Mista Santos da Shugaban Farc Timoleon Jimenez, wanda aka fi sani da Timochenko, za su sanya hannu kan yarjejeniyar.
Sai dai ya ce za a dauki dogon lokaci kafin jama'ar Colombia su farfado daga yakin da aka shafe fiye da shekaru 50 ana gwabza wa.
Za a sake kafa kungiyar ta Farc a matsayin jam'iyyar siyasa a wani bangare na yarjejeniyar.
A ranar 2 ga watan Oktoba ne al'umar kasar za su kada kuri'ar raba-gardama kan shirin da aka cimma da kungiyar ta Farc.
"Da babu wannan yakin, da tattalin arzikinmu zai iya bunkasa da kashi biyu ko uku cikin dari a shekaru 23 da suka gabata," kamar yadda Mista Santos ya shaida wa wakiliyar BBC Lyse Doucet.
Sannan ya ce yakin ya yi mummunar tasiri ga al'umar kasar.
Shugaban ya kara da cewa "duk kasar da ta shafe shekaru 50 tana yaki, to hakika ta ruguza dukkan wasu dabi'unta".
Asalin hoton, Inpho
Kungiyar Farc na yakar gwamnatin Colombia tun shekarar 1964