Farfaganda kawai Shekau yake yi- Sadiq

Farfaganda kawai Shekau yake yi- Sadiq

A Najeriya, rundunar sojin sama ta kasar wadda a baya ta yi ikirarin raunata shugaban daya daga cikin bangarorin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a wani hari ta sama, ta ce yanzu haka jami'anta na nazari kan sahihancin faifan bidiyon da ya fitar yana karyata raunata shi. A wata hira da Haruna Shehu Tangaza, babban hafsan rundunar, Air Marshal Sadik Baba Abubakar ya ce farfaganda Shekau ya ke yi.