An yi zazzafar mahawar tsakanin Hillary da Trump

Sama da mutane miliyan dari ne suka kalli muhawarar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da 'yan takarar suka yi mahawara

An gudanar da zazzafar mahawara mai cike da kalubalantar juna tsakanin 'yan takarar shugabancin Amurka wato Hillary Clinton da kuma Donald Trump.

Mr Trumph ya rinka tsomawa Mrs Clinton baki a lokacin da take magana yana mai kalubalantarta akan haifar da matsaloli da dama a kasar a lokacin da take gwamnati.

Ya kuma ce bata da kwarewa da kuma dabarun da zata iya zama shugabar kasa.

Manyan 'yan takarar biyu, sun fafata kan batutwua da dama, da suka hadar da samar da ayyukan yi, da batun ta'addanci, da kuma wariyar launin fata.

An kiyasta cewa sama da mutane miliyan 100 ne suka kalli mahawarar a fadin duniya.

A wasu lokutan dai an yi amfani da sukar mutuntaka, inda Trump ya zargi abokiyar karawar sa Hilary da cewa ba ta da kwarjinin da zata zama shugabar Amurka.

Ita ma dai Clinton ta durarwa Trump da cewa ya ki sakin bayanan biyan haraji.

To sai dai hamshakin dan kasuwar ya ce zai futar da bayanan harajin nasa idan abokiyar hamayyar sa Clinton ta saki sakonnin imail dubu 33 da ta goge yayin da ake binciken ta lokacin da ta ke sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Hillary ta kuma soki Trump sabo da yabon shugaban Rasha Vladmir Putin.

'Yan takarar biyu sun yi musayar kalamai kan batun cewa musulman Amurka sun zama barazana.

Mahawarar dai ita ce ta farko da yan takarar biyu suka yi gabanin zaben da za a yi ranar 8 ga watan Nuwamba.