Hukumar kwallon kafa ta Ingila zata binciki Sam Allardyce

Ingila za ta binciki Sam Allardyce
Bayanan hoto,

Hukumar kwallon kafa ta Ingila zata binciki Sam Allardyce

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, za ta binciki kociyan tawagar kwallon kafarta Sam Allardyce, bisa zargin cuwa-cuwa kan cinikin dan kwallo.

Ana zargin Allardyce da yin amfani da damarsa inda ya shirya cuwa-cuwar da ta kai fam 400,000 ya kuma bayar da shawarar yadda za a kaucewa bin ka'idar sayar da dan was an tamaula.

Telegraph ta ce tana da bidiyon da Allardyce ya yi taro a cikin watan Agusta da wasu mutane, inda ya sanar da su yadda za a bi a kaucewa ka'ida domin biyan bukata.

Allardyce mai shekara 61, bai ce komai ba kan zargin, yayin da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bukaci da a bata faifan bidiyon domin ya zama hujja.

Allardyce tsohon kociyan Sunderland ya maye gurbin Roy Hodgson a cikin watan Yuli a matsayin kociyan tawagar kwallon kafa ta Ingila.