Suarez ya fara wasannin bana da kafar dama bayan da ya ci kwallaye takwas

Suarez ya fara wasannin bana da kafar dama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Suarez ya fara wasannin bana da kafar dama bayan da ya ci kwallaye takwas

Luis Suarez ya fara yin wasannin kakar bana da kafar dama, bayan da ya ci kwallaye takwas a wasanni tara da ya yi wa Barcelona.

Dan kwallon tawagar Uruguay ya fara ci wa Barca kwallo a karawar da kungiyar ta doke Sevilla a wasan Spanish Super Cup da suka yi a ranar 14 ga watan Agusta.

Suarez ya kuma ci kwallaye uku a wasan da Barcelona ta ci Real Betis 6-2 a gasar La Liga, a dai wasannin La Ligar ya ci Leganes da Sporting Gijon kwallaye daidai..

A karawar da Barcelona ta casa Celtic da ci 7-0 a gasar cin kofin zakarun Turai, Suarez ya zura kwallaye biyu a raga a fafatawar.

Dan wasan shi ne ya lashe kyautar wanda ya fi cin kwallaye a gasar La Liga ta bara, inda ya ci 40, a bana kuwa ya ci kwallaye biyar a gasar da shi da Antoine Griezmann na Atletico, bayan da aka yi wasanni shida.

Barcelona za ta ziyarci Jamus a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba, inda za ta kara da Borusia M. Gladbach.