Za a taimakawa mata da ba sa haihuwa a Nigeria

Asalin hoton, Getty Images
Za a taimakawa matan da sana'o'i da magunguna
Katafaren kamfanin hada magungunan nan na Merck tare da hadin gwiwar wata kungiyar ta matar shugaban Najeriya, Aisha Buhari za su kaddamar da wani shiri a Abuja, domin taimakawa matan da ba sa haihuwa.
Za a samarwa matan tallafin sana'o'i da kuma shawarwari da magungunan matsalar ta rashin haihuwa.
Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta cewa kimanin ma'aurata miliyan 180 ne ke fama da matsalar rashin haihuwa a kasashe masu tasowa.
Kuma a nahiyar Afrika cututtuka ne ke haddasa kimanin kashi 85 cikin dari na matan da ke fuskantar matsalar rashin haihuwa, idan aka kwatanta da kashi 33 cikin dari na duniya.