B M'gladbach za ta kara da Barca a gasar zakarun Turai

Borussia Munchen Gladbach

Asalin hoton, Getty Images

Borussia Munchen Gladbach za ta karbi bakuncin Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai a wasa na biyu na cikin rukuni da za su yi a ranar Laraba.

Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu za su fafata a tsakaninsu, kuma Lionel Messi ba zai buga karawar ba, sakamakon jinya da yake yi tare da Samuel Umtiti.

Barcelona ta ci Celtic 7-0 a wasan farko da ta yi a gasar, yayin da Mgladbach ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 4-1.

Haka kuma Barcelona ta doke Leganes da ci 5-1 sannan ta casa Sporting da ci 5-0 a wasannin La Liga biyu na baya-bayan nan da ta yi.