Kevin de Bruyne zai yi jinya zuwa mako uku

De Bruyne zai yi jinyar mako uku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kevin de Bruyne na haskaka wa a Manchester City

Kociyan Manchester City, Pep Gaurdiola, ya ce Kevin de Bruyne zai yi jinya zuwa mako uku masu zuwa.

De Bruyne ya yi rauni ne a karawar da Manchester City ta doke Swansea da ci 3-1 a gasar Premier da suka yi a ranar Asabar.

Guardiola ya kuma sanar da cewar Kyaftin din kungiyar Vincent Kompany, na daf da dawowa murza-leda nan da mako biyu ko uku masu zuwa.

City tana sa ran De Bruyne zai dawo buga tamaula a karawar da kungiyar za ta fafata da Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar 19 ga watan Oktoba.