Nigeria: Al'umar Borno na bukatar agajin gaggawa - MSF

Nigeria: Al'umar Borno na bukatar agajin gaggawa - MSF

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Borno na bukatar agajin gaggawa - MSF

Kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres (MSF), ta ce ana bukatar kayan agaji masu yawa cikin gaggawa a yankunan karkara da kuma babban birnin jihar Borno, Maiduguri.

Ta ce matsananciyar halin rayuwa da 'yan gudun hijira ke ciki ta fi azabartarwas da yakin Boko Haram da ya raba su da gidajensu ya yi musu.

A wani rahoto da ta fitar a ranar Laraba, MSF ta ce wannan lamari na yin mummunar tasiri kan 'yan al'umar jihar.

A cewar rahoton, "mutane sun fake a garuruwa ko kuma sansanonin da ke karkashin sojoji, kuma sun dogara ne kacokan kan kayan agajin da ba sa isa wurinsu".

Sama da mutane 20,000 ne suka mutu a shekaru bakwai da aka shafe ana rikicin Boko Haram, sannan sama da miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.

"Duk da an kadamar da shirin bayar da abinci mai gina jiki watanni uku da suka wuce, an kasa taimakawa mutanen Borno," a cewar Hugues Robert, shugaban kula da agaji na MSF.

Ya kuma kara da cewa "Muna kira da a kawo kayan agaji ba tare da bata lokaci ba".

A ranar 19 ga watan Satumba ne dai MSF din ta je garin Ngala, inda 'yan gudun hijira 80, 000 ke zama wadanda "duniya ma ba ta san da su ba".

Kungiyar ta ce "ba su da abinci da magunguna".

A cewarta, 'yan gudun hijirar sun makale a sansanin, kuma ba za su iya tafiya ba.

Wani bincike da aka yi akan abinci mai gina jiki na yara sama da 2,000 da ke kasa da shekara biyar, ya gano cewa daya a cikin yara 10 na fama da matsananciyar yunwa da ke barazana ga rayuwarsu.

Mutane a sansanin sun rawaito cewar kowanne mutum daya na samun rabin lita na ruwa ne kawai a ko wacca rana.