Amurka ta kori wanda ake zargi da hannu a kisan kare-dangi

Kwarangwal din kawunan wadanda aka kashe a yakin basasar Rwanda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A karon farko a Afirka, an kashe mutane kusan 800,000 a kisan kare dangin kasar Rwanda

Gwamnatin Amurka ta kori wani malamin makaranta dan kasar Rwanda, wanda ake zargin yana daga cikin muhimman mutanen da suka haddasa kisan kare-dangi na shekarar 1994 daga kasar.

Korar da aka yi wa Leopold Munyakazi ta zo ne bayan da ya kasa yin nasara a fafutikar da ya ke yi ta neman mafaka a Amurkar.

An zarge shi da saka ganyen ayaba a jikinshi a lokacin kisan kare-dangin domin ya bayyana kanshi a matsayin dan kabilar Hutu da kuma shirya hare-hare da daddare a kan gidajen 'yan kabilar Tutsi da ke gaba da 'yan kabilar Hutu.

Sai dai Mista Munyakazi, wanda tsohon farfesa ne, ya musanta zargin.

Mayakan sa kai sun yi wa 'yan kabilar Tutsi 800,000 da kuma 'yan kabilar Hutu masu matsakaicin ra'ayi yankan rago a kwanaki 100 kawai a shekarar 1994.

A shekarar 2004 ne dai Mista Munyakazi ya gudu ya je Amurka.

Tuni dai kasar Rwanda ta bukaci a tasa keyar Munyakazi, tana tuhumar shi da laifukan kisan kare-dangi da kuma hada baki a boye domin aiwatar da kisan kare-dangi.

Hukumar da ke yaki da kisan kare-dangi, wadda ke da goyon bayan gwamnati, ta zarge shi da bai wa mayakan sa kai na kabilar Hutu umarni su kamo 'yan kabilar Tutsi su kuma harbe wani mutum da ake kira Ugirashebuja Felicien a yankin Kirwa da ke kudu maso gabashin kasar ta Rwanda.

Hukumar ta kuma zarge shi da haddasa kiyayya da kuma rubuta wani labari da ya yi kira da a bai wa 'yan kabilar Tutsi wakilcin kashi 10 cikin 100 kawai a makarantu da ma'aikatu.

Mista Munyakazi dai ya dage cewar shi dan kabilar Hutu ne mai matsakaicin ra'ayi wanda ya taimaka wa 'yan kabilar Tutsi a lokacin kisan kare-dangin.