Ethiopia: An kaddamar da layin dogo na zamani zuwa Djibouti

Akalla kashi 90 cikin dari na duk hada-hadar kasuwancin Habasha na bi ta kasar Djibouti
Kasar Habasha na shirin kaddamar da wani layin dogo mai amfani da wutar lantarki, wanda zai hada Addis Ababa, babban birnin kasar da tashar jirgin ruwan Red Sea da ke kasar Djibouti.
Ana ganin wannan zai yi matukar habbaka tattalin arzikin kasashen biyu.
Jiragen kasan za su yi tafiyar kilomita 750 cikin sa'o'i goma, tafiyar da kan dauki kwana-da-kwanaki ta mota.
Wasu kafanonin kasar China ne biyu suka gina layin dogon a kusan dala biliyan uku da miliyan 400.
Kuma ma'aikatan kasar Sin din ne za su rika gudanar da aikin jirgin kasan.
Akalla kashi 90 cikin dari na duk hada-hadar kasuwancin Habasha na bi ta kasar Djibouti.

Kamfanonin China ne suka ginalayin dogon

Jiragen kasan za su yi tafiyar kilomita 750 cikin sa'o'i goma