Shugabanni sun yaba wa Shimon Peres

Jana'izar Shimon Peres

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugabanni da dama sun halarci jana'izar Shimon Peres

Shugabannin duniya sun yabi irin abubuwan tarihi da tsohon shugaban kasar Isra'ila, Shimon Peres, ya bari a lokacin jana'izarsa da aka yi kwanaki uku bayan mutuwarsa.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba yana da shekara 93 a duniya.

A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a taron makokin, Firai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana shi a matsayin "Jarumi".

Shugaban Amurka, Barrack Obama, ya ce halartar makokin da shugaban Falasdinu, Mahmooun Abbas ya yi wata "Tunasarwa ce kan cewa ba a kawo karshen yunkurin samun zaman lafiya mai dorewa a tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba".

Mista Abbas dai na daya daga cikin manyan bakin da suka halarci taron makokin daga kasashen waje.

An tsaurara matakan tsaro gabannin jana'izar, lamarin da ya kai ga kama mutane da dama.

A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa mai sosa rai, Mista Netanyahu ya ce yayin da Isra'ila da kuma duniya ke alhinin rashin Mista Peres, akwai kyakkyawan fata saboda ayyukan da ya bari.