'Jahilci ne babbar matsalar Fulani'

Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya
Bayanan hoto,

Fulani dai na fama da tashe-tashen hankali da sauran kabilu

Wasu 'yan kabilar Fulani a Najeriya, sun ce jahilci ne ya jefa al'ummar Fulani a halin da suke ciki a yanzu haka.

Mutanen dai sun yi zargin cewa an mayar da Fulani Saniyar-ware a fannonin ilimi da na cigaba, al'amarin da ya sanya ba su san komai ba sai yawan tashin hankali.

To sai dai Fulanin sun dora alhakin hakan ne a kan shugabanninsu musamman ma na kungiyar Miyetti Allah wadda ke kula da makiyaya.

Abin da Fulani ke so dai shi ne a sanya su cikin tsarin makarantun zamani da na addini sannan kuma a ware mu su wuraren da dabbobinsu za su samu cimaka.

Hakan a cewarsu zai taimaka wajen wayar da kan Fulanin su zauna lami lafiya da sauran kabilu.

To sai dai shugabannin Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta ce ba haka lamarin yake ba.

Shugaban Miyetti Allah na jihar Kaduna, Hardo Alhaji Usman, ya ce idan ma haka batun yake, to sun gaje shi ne daga shugabancin da ya gabata.