'Gwamnatocin baya ne suka lalata tattalin arzikin Nigeria'

Shugaban ya tabo batutuwa da dama kan cigaban kasa
Bayanan hoto,

Buhari ya yi jawabin ne lokacin cikar Najeriya shekara 56

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatocin baya ne suka jefa kasar a halin da take ciki na matsalar tattalin arziki.

Buhari ya fadi hakan ne a wani jawabi da ya yi wa 'yan kasar da safiyar Asabar, a wani bangare na cikar Najeriyar shekara 56 da samun 'yancin kai.

Shugaban ya ce rashawa da cin hanci da suka yi katutu a gwamnatocin baya ne ummul'aba'isin halin da ake ciki.

Ya kuma kara da cewa tayar da kayar bayan da tsagerun Niger Delta ke yi, ya taimaka gaya wajen fadawar kasar cikin wannan yanayi.

Sai dai kuma shugaba Buhari, ya ce ya yi imanin halin da ake ciki na wani dan lokaci ne.

Dangane da sha'anin tsaro, Buhari ya ce tun a watan Disambar 2015 ne sojojin kasar suka karya lagon kungiyar.

Amma ya ce har yanzu ana samun hare-haren sari-ka-noke nan da can a jihar Borno.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shugaba Buhari ya ce a kudurin gwamnatinsa na bunkasa hanyoyin sufuri, tuni an fara ayyukan gyara da tagwaita wasu manyan titunan kasar nan da suka hada da;

titin Kano zuwa Katsina wanda za a tagwaita, da Hadejia zuwa Nguru, da Kano zuwa Maiduguri, da Azare zuwa Potiskum.

Akwai kuma titin Ilori zuwa Jebba ya bi Mokwa ya je Birnin Gwari, da na Lokoja zuwa Benin, da Legas zuwa Badun, da Anacha zuwa Enugu ya wuce Anambara, da sauransu.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen farfado da manyan tafkuna 12 da ke fadin kasar nan sannan kuma za ta mika su ga 'yan kasuwa ta yadda Najeriya za ta koma amfani da hanyoyin noman rani maimakon dogaro da ruwan damuna.

A fannin bunkasa wutar lantarki, Shugaba Buhari ya ce gwamnati na kokarin bullo da hanyoyin samar da lantarki ta hasken rana da ruwa da kuma iska, sannan tana hada hannu da kasar China don inganta sashen, kuma an bayar da umarnin kammala ayyukan samar da lantarki a karkar.