An kori alkali saboda ya ki amincewa da auren jinsi daya

Roy Moore

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mutanen da dama na goyon bayansa

An dakatar da babban alkalin kotun Alabama da ke Amurka har karshen wa'adinsa saboda ya ki bin hukuncin kotun tarayya na halatta auren jinsi daya.

Alkaki Roy Moore, mai shekara 69, ya sabawa ka'idojin sharia'a inda ake ganin ya bayar da wani umarni da ke sa alkalan da ke kasa da shi su ki bayar da lasisi ga masu auren jinsi daya.

Alkalin ya ce an dakatar da shi ne domin cimma wata manufa ta siyasa, yana mai shan alwashin kalubalatar matakin a gaban kotu.

Wannan ne karo na biyu da ake dakatar da Mr Moore, wanda mutanen ne da ya yi fice wajen bayyana ra'ayin na 'yan-mazan-jiya.

A shekarar 2003, an tsige shi daga mukaminsa saboda ya ki cire wata alama ta shika-shikan addinin Kirista da ya sanya a ginin kotunsa.