Haraji: Indiya ta gano $10b na boye

Narendra Modi na India
Bayanan hoto,

Narendra Modi, ya yi alkawarin samar da biliyoyin dala ta yaki da almundahana, da aka zabe shi a 2014.

Dubun dubatar jama'a ne a Indiya suka bayyana kusan dala biliyan 10 na kudaden da suka mallaka a boye, a karkashin wani shirin gwamnati na yin afuwa ga masu kin biyan haraji.

Wadanda ake zargi da kin biyan haraji sun yi ta tururuwa suna gabatar da kudadensu, yayin da wa'adin da gwamnti ta diba na wata hudu ya kare ranar Juma'a.

Wadanda suka amsa kiran gwamnati suka bayyana kudaden nasu da suka boye da ba sa biya musu haraji, ba za a tuhume su ba a kotu, amma za su biya harajin kashi 45 cikin dari na kudaden.

Kudaden da mutane ke samu wadanda suke kin bayyana wa gwamnati su don kauce wa haraji, ana kiransu da bakin kudi (black money).

Badakalar ta yi kamari sosai a kasar ta Indiya, inda kusan kashi uku cikin dari ne kawai na mutanen kasar biliyan daya da miliyan 200 ke biyan harajin kudaden da suke samu.

Gwamnati ta ce za ta kashe kudaden da za ta tattara daga shirin afuwar a fannin jin dadin jama'a.

Firai ministan Indiyan Narendra Modi, ya dauki wannan matakin ne a matsayin wani shiri na cika alkawarin cewa zai yi yaki da cin hanci da rashawa, lokacin da ka zabe shi a 2014.