'Ina kuɗaɗen da Buhari ya ce ya kwato daga barayin gwamnati?

An dade ana mahawara kan kudaden da aka yawansu ya wuce Naiara Tiriliyan Uku
Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya ce ya killace makudan kudaden da ya kwato daga hannun barayin gwamnati

Daya daga cikin kananan jam'iyyun adawa a Najeriya, National Conscience Party, ta ce ba za ta amince da shirin gwamnatin tarayya ba na cefanar da wasu kadarorin kasar da manufar farfado da tattalin arziki.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Dr. Yunusa Tanko ya bayyana hakan, a yayin taron jam'iyyar na kasa a birnin Legas, ranar Asabar.

Dr Tanko ya ce idan dai har gaskiya ne cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta tara fiye da Naira Tiriliyan uku ,to mai zai hana yin amfani da kudaden wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Gwamnatin Muhammadu Buhari dai ta ce ta samu nasarar tara makudan kudade sakamakon kwato kudaden daga hannun mutanen da suka yi sata daga lalitar talakawa.

Wata hanyar da gwamnatin ta ce ta tara kudaden ita ce samar da Asusun bai daya na TSA wanda ya janyo tsuke bakin aljihun gwamnatin daga zirarewa.

Dr. Yunusa Tanko ya kara da cewa idan har gaskiya ne an tara kudade masu yawa haka to babu ma bukatar a ciyo bashi daga wani wuri domin cike gibin kasafin kudin kasar.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin shugaba Buhari take ta godon ganin ta magance karayar tattalin arzikin da kasar ta samu.