Kila Trump ya zille wa biyan haraji

An sha sukar Donald Trump kan kin bayyana harajinsa

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Game da zargin kin biyan haraji da Clinton ta yi masa, Donald Trump ya ce, ''wannan shi ya sa na zama mai wayo''

Wata jaridar Amurka ta ce ta samu takardu da ke nuna cewa dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya yi asarar sama da dala miliyan 900 a takardun harajinsa na 1995.

Jaridar New York Times ta ce asarar na da girman gaske da ke nuna cewa dan takarar ka iya kwashe shekara goma sha takwas ba tare da biyan wani haraji ba.

Kawo yanzu dai kwamitin yakin neman zaben Trump bai ce komai ba dangane da girman asarar dan takarar a harkokin kasuwancinsa ba kuma bai gabatr da takardr bayanan harajinsa ba.

Sai dai kuma a wata sanarwa, kwamitin ya ce mista Trump kwararren dan kasuwa ne wanda ya san dokokin haraji fiye da duk wani da ya taba tsaya wa takarar shugabancin Amurka.

Abokiyar hamayyar Donald Trump, Hillary Clinton ta sha sukarsa kan kin bayyana takardun harajinsa