'Yan sandan Habasha sun kara da masu bore

Asalin hoton, Getty Images
Masu zanga-zanga na kyamar yadda ake tafiyar da gwamnati.
Rahotanni daga kasar Habasha na cewa mutanen da dama sun mutu a yayin wani turmutsutsu yayin da 'yan sanda suka yi taho-mu-gama da masu kyamar yadda gwamnati ke tafiyar da al'amuran kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani ganau na cewa 'yan sanda sun yi ta harbe-harbe, da fatattakar masu boren ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye a wajen wani bikin al'adun gargajiya da ake yi a garin Bishoftu da ke yankin Oromiya.
Yankin Oromiya da jihar Amhara sun yi ta fama da tashe-tashen hankula a 'yan watannin da suka gabata.
A tashin hankali na baya-bayan nan da ya faru kusan mutane dari ne suka rasa rayukansu, yayin wani bore da aka yi na kin jinin yadda gwamnatin kasar ke tafiyar da mulki.
Sai dai a nasu bangaren hukumomin kasar na cewa, makarkashiya ce ake kullawa daga kasashen ketare.