A hana fataucin Aku mai magana dake Afirka

Asalin hoton, Gwent Police
Aku mai kwaikwayon maganar mutane
Wakilai a wajen taron kare dabbobin daji na duniya sun amince a hana fataucin Aku mai launin toka dake nahiyar Afirka.
Sun amince da matakin ne a wajen taron kare halittu da rayuwarsu ke cikin hadari wanda ke gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.
Ana matukar bukatar irin Akun, saboda basirar shi ta kwaikwayon maganar mutane.
A 'yan shekarun nan amma, yawan Akun a Afirka ya ragu saboda farautarsu da lalata dazuzzuka da ake yi.
Kungiyar kare dabbobin daji ta duniya-WWF, ta yi maraba da matakin, inda ta bayyana shi a matsayin wani babban hobbasa na kare tsuntsayen.
Yarjejeniyar wacce kasashe fiye da dari biyu suka rattaba mata hannu, za ta kare dabbobi fiye da dubu biyar da wasu nau'o'in bishiyoyi dubu talatin, daga barazanar kasuwancinsu.