'Yan bindiga sun kashe sojan Kamaru

Cameroon soldiers
Bayanan hoto,

Sojojin Kamaru masu sintiri

Rahotanni daga Kamaru na sun ce an kashe sojan kasar guda, tare da raunata wasu biyu a wani hari da aka kai a garin Dambore-Ardebe dake Makary a yankin Arewa mai Nisa na kasar.

Acewar rahotannin, majiyoyin sojin kasar sun ce wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne, dauke da muggan makamai sun kai hari karamin barikin sojin ruwa dake Dambore-Ardebe.

Rahotannin sun kara da cewa 'yan bindigan sun kwashi makamai daga barinkin sojin, sannan suka cinna mushi wuta.

Makary dai, ya na kan iyaka ne da Najeriya, kuma mayakan Boko Haram na yawan kai masu hari.