An kori Rahama Sadau daga Kannywood

Rahama ta yi fice a fina-finan Kannywood
Kungiyar 'yan fim ta Kannywood a Najeriya ta kori fitacciyar jarumar nan Rahama Sadau saboda wakar da ta yi inda ta rungume abokin wakar ta ta.
A faifan wakar, wacce ita ce ta farko da jarumar ta yi da harshen Turanci, an nunota tana rungume mawaki "Classiq" sannan tana kwanciya a jikinsa.
Kakakin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa Balarabe Bahru, ya tabbatar wa da BBC matakinsu na korar jarumar.
Jama'a da dama sun yi Allah-wadai da ita, yayin da wasu tsiraru suka yaba mata.
Kawo yanzu dai jarumar, wacce take kasar India ba ta ce komai ba.
Ba wannan ne karon farko da take jawo ce-ce-ku-ce ba