'Talauci na raguwa a duniya'

Bankin Duniya na son cimma daidaito a 2030
Bayanan hoto,

Bankin Duniya ya ce dole sai an rage rashin daidaiton da ke tsakanin masu arziki da matalauta

Babban Bankin Duniya ya ce an samu raguwar matsananci talauci a daukacin duniya, duk kuwa da tafiyar hawainiyar da tattalin arziki ke yi wajen habaka.

Yawan mutanen da aka ayyana a matsayin matalauta na innanaha a shekarar 2013 sun kai miliyan dari takwas.

Hakan na nufin an sami ragin mutane miliyan dari daya, idan aka kwatanta da yawan matalautan a shekarar da ta gabaci 2013.

Bankin na duniya ya ce an samu cigaba a nahiyar Asia musamman ma kasar Sin da Indonesia da kuma India.

Sai dai Bankin ya yi gargadin cewa akwai bukatar kara zagewa wajen kawar da wagegiyar tazarar da ke tsakanin masu shi da matalauta.

Bankin ya kuma kara da cewa cimma burin bankin na kawo karshen talauci a fadin duniya a shekara 2030, ya ta'allaka ne ga kawar da rashin daidaiton da ke tsakanin mutane.