Saudiyya ta koma amfani da shekarar Bature

King Salman, Saudi Arabia

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Sarki Salman na Saudiyya na daukar matakan tsuke bakin aljihu tun faduwar farashin mai a 2014

Saudi Arabia ta daina amfani da kwanan watan Musulunci inda ta koma amfani da na Turawa wajen tsarin biyan albashi da dukkanin kudaden ma'aikatanta a wani mataki na tsuke bakin aljihunta.

Tun a ranar Laraba majalisar ministocin kasar ta amince da sauyin, amma kuma sai a ranar Asabar 1 ga watan Oktoban nan aka fara aiwatar da tsarin.

Ita dai shekarar Hijiriyya tana da watanni 12 masu kwanaki 29 ko 30, tare da kwanaki 354.

Yayin da shekarar Miladiyyar Annabi Isa wadda take da watanni 12 ita ma amma kuma masu kwanki 30 da 31, da jumullar kwanaki 365, ta zarta ta Musulunci da yawan kwanaki 11.

Saboda haka wannan bambancin kwanaki 11 ne yanzu ma'aikatan gwamnatin kasar za su rika yin aikinsu kenan ba tare da samun albashinsu ba, wanda hakan yake zaman wani mataki na rage kwanakin albashin ma'aikatan.

Wannan na daga matakan tsuke bakin aljihu da ta bullo da su, da suka hada da soke wasu kudaden alawus-alawus da ra-ra da take ba wa ma'aikatanta, tare kuma da kara yawan kudaden neman takardar izinin shiga kasar (visa) ga baki da kuma mazauna Daular.

Sarkin Salman na Saudiyyar ya kuma bayar da umarnin rage kashi 20 cikin dari na albashin ma'aikatan gwamnatin, yayin da su ma 'yan majalisar tuntuba ta kasr aka rage musu kashi 15 cikin dari na kudin da ake biyansu.

Kudin da Saudiyya wadda ita ce ta daya a duniya wajen fitar da man fetur take samu sun ragu tun 2014, lokacin da farashin mai ya yi kasa.

Daular ta fara amfani da kalandar hijiriyya ne tun lokacin da aka kafa ta a 1932.