Habasha na alhinin mutane a kalla 52 da suka mutu

'Yan Habasha a lokacin da suke zanga zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Habasha na alhinin kwana uku

'Yan kasar Habasha na alhini na kwanaki uku bayan a kalla mutane 52 sun rasa rayunkansu a lokacin wata zanga-zanga a wurin wani bikin al'adun gargajiya a lardin Oromio a ranar Lahadi.

A halin yanzu dai ana cece-kuce a kan abinda ya haddasa mace macen.

A wata sanarwa da gidan talbijin din Habashar ta fitar, ta ce ana alhinin mutuwar 'yan kasa, wadanda ba su ji ba basu gani ba kuma suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da marasa son zaman lafiya suka haddasa.

Sai dai Firai Minista, Hailemariam Desalegn ya dora alhakin rikicin, wanda ya jawo turmutsutsu, kan masu zanga-zangar.

'Yan adawa, sun ce jami'an tsaro ne suka haddasa turmutsutsun a lokacin da suka harba hayaki mai sa hawaye da harsasai kan mutane masu yawa wadanda suka taru domin bikin al'adar gargajiya.

Sun kuma kara da cewar yawan mutanen da suka mutu sun fi yawan alkaluman 52 da aka fitar a hukumance.