An ceto 'yan gudun hijrar Libya 6000

Libya migrants
Bayanan hoto,

Wadannan na daga 'yan gudun hijra mafiya yawa da aka ceto a lokaci daya

Jami'an tsaron gabar teku na Italiya sun ce an ceto 'yan gudun hijira kusan dubu shida daga teku ranar Litinin.

Wannan shi ne daya daga cikin aikin ceto na 'yan gudun hijira da yawa a lokaci a kuma rana daya.

Mutanen suna cikin jiragen ruwa ne kusan 40 da aka makare su da jama'a, wadanda suka taso daga Libiya.

Jami'an tsaron na Italiya sun tsamo gawarwaki na mutane tara a cikinsu.

Jami'an sun kuma ce akwai jirgin ruwa daya da ke dauke da mutane sama da 700, wadanda kusan 200 yara ne.