'Ba a yi wa Rahama Sadau adalci ba kan korar ta'

Rahama Sadau ta dare bayan Classiq a sabon faifan bidiyon wakarsa da ya fitar mai suna "I Love You"
Bayanan hoto,

MOPPAN ta ce rungumar Classiq da Rahama Sadau ta yi ta saba da ka'idojin kungiyar

Mutane a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da hukuncin korar fitacciyar 'yan fim din nan, Rahma Sadau, da kungiyar masu fina-finan Hausa ta yi bisa rungumar wani mawaki.

A wani jin ra'ayin jama'a da wakilinmu na Kano, Mukhtar Adamu Bawa ya yi, yayin da wasu ke cewa hukuncin ya yi dai-dai, wasu kuwa na cewa ko alama ba a yi mata adalci ba.

Masu wannan ra'ayi dai na cewa ba a yi wa Rahama adalci ba sun jingina dalilinsu ne kan abubuwa guda biyu:

  • Ba a ji ta bakin 'yar fim din ba aka kore ta.
  • Ba Rahma Sadau ba ce kadai take irin wannan dabi'a ba domin ai maza kamar irin su Ali Nuhu da Sani Danja sun aikata abubuwan da suka fi nata girma.
  • Korar Rahma Sadau daga fina-finan Hausa ka iya sanya ta koma yin fina-finan Turanci abin da ke nuni da cewa garin neman gira za a iya rasa ido.

To sai dai Kungiyar Masu Hada Fina-finan Hausa wato MOPPAN ta ce ai yanzu ne ta fara aiki.

Ta kara da cewa hukunta Rahma Sadau an yi ne domin ya zama izna ga duk mai son yin irin wannan a nan gaba.

A ranar Lahadi ne dai kungiyar ta MOPPAN ta sanar da korar 'yar wasan daga sake taka duk wata rawa a harkar fina-finan Hausa.

MOPPAN dai ta ce halayyar da Rahma Sadau ta nuna ta saba da halayyar Hausawa da kuma addinin Musulunci.

Sai dai kuma kungiyar ta ba wa jarumar kwanaki 30 da ta bayyana a gabanta domin kare kai.

A ranar Litinin ne kuma aka bude wani sabon maudu'u a shafukan sada zumunta da ke kalubalantar hukuncin da kungiyar ta dauka a kan 'yar wasan.