Amnesty ta yi Allah-wadai da kasashe mafiya arziki

'Yan gudun hijirar Syria a Jordan

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wasu daga dubban 'yan gudun hijirar Syria kenan a Jordan

Kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya ta Amnesty International, ta caccaki kasashen duniya mafiya arziki bisa kin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kan 'yan gudun hijira.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da attajiran kasashen ne tana cewa, su ne ke karbar mafi karancin 'yan gudun hijirar sannan kuma su ne ke yin abin da bai taka kara ya karya ba.

Babban Sakataren kungiyar Salil Shetty, ya ce yanayin zai kazanta, har sai kowacce daga cikin kasashen mafiya arziki sun karbi yawan 'yan gudun hijira daidai da girmanta da dukiyarta da kuma guraben aikinta.

A rahoton da kungiyar ta Amnesty ta fitar, ta ce sama da 'yan gudun hijira miliyan 21 na duniya na tsugune ne a kasashe 10 kawai.

Ta farko ita ce Jordan, mai yawan al'umma kasa da miliyan takwas, amma kuma ta karbi 'yan gudun hijirar Syria sama da dubu 600.