Alkalin Najeriya ya musanta karbar hanci

EFCC
Bayanan hoto,

Zargin cin hanci ya yi katutu a fanni shari'a

A Najeriya daya daga cikin manyan alkalan da majalisar kula da lamurran shari'a ta kasar ta dakatar bisa zargin karbar hanci, ya ce zargin da aka yi masa ba gaskiya ne ba.

Justice Mohammed Ladan Tsamiya wanda kafin dakatar da shi, shi ne alkalin kotun daukaka kara da ke birnin Ilori ya ce a cikin sakon da majalisar ta NJC ta aike masa babu inda ta ce an same shi da laifin karbar hanci na miliya 200.

''NJC ta aiko min da sakamakon bincikenta da kuma shawarwarinta; babu inda aka ce an samu shaida cewa an bani hanci,'' inji Mai shari'a Tsamiya a wata hira da BBC.

Kodayake dai bai musanta cewa an dakatar da shi ba, amma ya ce yadda kafafen watsa labarai suka bayar labarin akwai kuskure a ciki.

A ranar Jumu'a dai ne majalisar kula da lamurran shari'a ta kasar (NJC) ta sanar da dakatar da wasu alkalan kotun daukaka kara biyu ciki har da Justice Tsamiya, ta kuma bayar da shawarar sallamar wani alkalin babbar kotu a jihar Kano bisa samunsu da laifuka daban-daban na karbar rashawa.