Me ke hana gudanar da zaben gaskiya a Najeriya?
- UmmulKhairi Ibrahim
- BBC Hausa, Abuja

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Nigeria ta kaddamar da wani kwamiti karkashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawan kasar Senata Ken Nnamani domin gano hanyoyin da za a yi garambawul a tsarin zaben kasar.
Gwamnatin dai ta ce nazarin da ta yi kan babban zaben da aka yi a kasar bara da wadanda suka gabace shi, shi ne yasa ta gano bukatar yin gyara domin gaba.
Kwamitin zai tattauna da masana da masu ruwa da tsaki a harkar domin bayar da shawarwari kan yadda za a tabbatar an gudanar zabuka masu adalci a kasar.
Sai dai ba wannan ne karo na farko da ake kafa irin wannan kwamiti ba, kuma wasu na ganin ba lallai ba ne ya sha bamban da na baya ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ce ke shirya manyan zabukan kasar
Amma a ina matsalar take?
Rashin dokoki ne ko kuwa kin aiwatar da su? Najeriya na da dokar zabe da ake amfani da ita wajen gudanar da dukkan zabubbuka.
Kuma kamar yadda yake a sauran kasashen duniya, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ce ke shirya manyan zabukan kasar.
Wadannan zabuka sun hada da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki na tarayya da kuma gwamnonin jihohi da 'yan majalisunsu.
Hukumar na da dokoki wadanda ta shimfida wa masu kaɗa kuri'a da kuma 'yan siyasa don tabbatar da an yi zabe karbabbe.
Sai dai daga bangaren 'yan siyasa da masu kaɗa kuri'a wani lokaci har da mahukunta ana karya dokokin zaben.

Asalin hoton, Getty Images
Dokar zabe ta kasa ta bai wa 'yan takarar shugabancin kasa damar kashe N1B
Kashe kudaden da suka wuce kima
A zabukan baya an zargi wasu manyan jam'iyyun siyasar kasar da kashe kudaden da suka wuce kima wajen yakin neman zaben.
Dokar zabe ta kasa sashi na 91 ta 2010, ta bai wa 'yan siyasar masu yakin neman shugabancin kasa damar kashe Naira biliyan guda, yayin da aka bai wa masu yankin neman zaben gwamna damar kashe miliyan 200.
Har ila yau dai, dokar ta tanadi hukunci ga 'yan siyasa, inda tace dan siyasa wanda ke yakin neman zaben shugaban kasa da ya kashe fiye da N1 biliyan zai fuskanci hukuncin daurin wata 12 a kurkuku ko kuma a ci shi tarar miliyan daya.
Yayin da mai yakin neman gwamna zai biya tarar naira 800,000 ko kuma ya sha daurin wata tara a gidan yari.
Sai dai a zahiri take cewa jam'iyyun siyasar kasar na kashe kudade fiye da yadda aka kayyade musu.

Asalin hoton, Getty Images
Ana zargin bangarorin siyasa da yin magudi
Magudi
Akwai zargin magudi da ake yiwa dukkan bangarorin siyasar kasar, inda a mafiya yawan lokuta suke amfani da matasa wajen sace akwatin zabe.
Wannan na bada damar yin aringizon kuri'u. Kuma shi ke haifar da rashin amince wa da sakamakon zaben da ake bayyana wa a karshe.
Ana zargin 'yan siyasar na amfani da kudi da ma kayan maye a wasu lokutan domin sa matasa aikata miyagun laifuka a lokutan zabe.
Amma duk da haka, da wuya ka ga an hukunta wani kan irin wannan aika-aikar.

Asalin hoton, Getty Images
Masana na ganin 'yan majalisu za su iya kawo gyara a harkar gudanar da zabe
Rawar majalisun dokoki
Wasu masana na ganin akwai rawa ta musamman da 'yan majalisun kasar za su taka wurin kawo gyara a wannan fanni.
"Su ne masu yin doka, a don haka su yakama su tabbatar cewa komai na tafiya yadda ya kamata,"a cewar Barrister Abdulhamid Muhammad, wani lauya mai zaman kansa a Abuja.
Ya shaida wa BBC cewa akwai dokoki a Najeriya, matsalar kawai ita ce rashin aiki da su.
Masu sharhi na ganin idan ana so a samu sauyi a yadda ake gudanar da zabuka a Najeriya, to dole ne jama'a da kuma 'yan siyasa su sauya dabi'unsu mussaman idan aka zo batun zabe.