Rigobert Song: Tsohon dan wasan Kamaru na jinya a Faransa

Rigobert Song

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Song ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Kamaru wasanni 137

An kai tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Kamaru, Rigobert Song, asibiti a kasar Faransa domin yi masa magani bayan ya farfado daga suman kwana biyu da ya yi.

A ranar Lahadi ne dai aka kai Song, mai shekara 40, babban asibitin da ke Yaounde, inda aka kwantar da shi bayan ya fadi ba a cikin hayyacinsa ba.

Ya yi ta dagawa magoya bayansa hannu a ranar Talata a wajen asibitin da ke Yaounde a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama.

Daraktan asibitin, Dakta Louis Joss Bitang A Mafok, ya ce Song ya kamu da ciwon "zubar jini a cikin kwakwalwarsa".

Dan uwansa Alexander, ya yi godiya ga irin soyayyar da 'yan Kamaru da magoya bayansa suka nuna.

"Danginmu na cikin wani mawuyacin hali. Mun ji dadi kwarai da irin soyayya da sakonnin da kuka isar.

Shi ma ministan lafiyar kasar Kamaru, Andre Mama Fouda ya bayar da na shi taimakon.

Song ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Kamaru wasanni 137, ya kuma taka leda a Liverpool da West Ham United.

Yanzu haka yana aiki a matsayin kociyan hukumar kwallon kafa ta Kamaru, bayan da ya bar aikin horar da kasar Chadi.