Safiyo Jama Gayre: Matar da ta yi jami'a tana da shekara 60

Safiyo Jama Gayre: Matar da ta yi jami'a tana da shekara 60

Babban burin Safiyo Jama Gayre a rayuwarta shi ne ta yi jami'a domin taimaka wa wadanda aka yi wa fyade da wadanda sauran matsalolin mata suka shafa a Somalia. Ta kuma je jami'a, inda ta karanci Shari'ar Musulunci da ta Nasara domin cimma burinta tana 'yar shekara 60.