Buhari zai mika jiragensa ga rundunar sojan sama

Jirgin Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jirage goma ne dai ake da su a fadar shugaban kasar.

Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari zai mika wasu karin jiragen samansa ga rundunar sojin sama ta kasar baya ga biyun da aka saka a kasuwa.

Da yake zantawa da BBC a babban birnin kasar Abuja babban mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai Malam Garba Shehu, ya ce daga cikin jiragen shugaban kasa akwai wadanda ake ganin za su amfani rundunar sojojin sama kuma za a aika ma ta da su.

'' Ana sa ra nan da 'yan kwanakkin da ke tafe kwamandan da ke kula da jiragen fadar shugaban kasa zai hadu da babban hafsan sojojin sama domin mika masa wadannan jiragen.'' In ji shi.

Rage yawan jiragen da shugaban kasar ke amfani da su dai na daga cikin alkawurran da shugaba Buhari ya yi kafin hawansa mulki a bara domin yin tsimin kudin da ake kashewa wajen kula da su.

Amma kuma shugaban ya ci gaba da amfani da garken jirage saman guda 10 da ya gada daga tsohon shugaba Goodluck Jonathan fiye da tsawon shekara daya; sai ranar Talata lokacin da aka sanar da matakin na sayar da biyu daga cikinsu.