Kungiyar al-Shabab ta kai hari a Kenya

Al-Shabab

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Al-Shabab tana adawa da gwamnatin Somalia

Gwamnan arewa maso gabashin Kenya ya ce wasu mahara da ake zargin 'yan kungiyar al-Shabab ne sun kashe akalla mutum shida a wani hari da suka kai a lardin .

Ali Roba, gwamnan lardin Mandera, ya kara da cewa mutum daya ya yi matukar jikkata sakamakon harin.

Amma ya ce jami'an tsaro sun ceci mutum 27 daga wurin da aka kai harin.

Jaridar Daily Nation ta kasar ta ce an kai harin ne da zummar kashe 'yan kasashen waje.

Al-Shabab tana yaki da gwamnatin Somalia wacce majalisar dinkin duniya ke mara wa baya kuma ta kai hare-hare da sau dama a Kenya.

Mayakan kungiyar sun sha kai hare-hare a lardin Mandera, wanda ke da iyaka da Somalia.

Jaridun kasar ta Kenya sun ce mayakan na harin 'yan kasashen waje ne a yawanci hare-haren da suka kai wa.