Rikicin Syria: IS ta kashe 'yan tawaye da dama

Shugaban 'yan tawayen na cikin wadanda suka mutu

Asalin hoton, LCC

Bayanan hoto,

IS ta taba kai hari a yankin a baya

Akalla mutane 29 wadanda akasarinsu 'yan tawaye ne suka rasa rayukansu a wani harin bam da kungiyar IS ta kai a kan iyakar Syria da Turkiya.

Harin ya afku ne a lokacin da ake musayar masu tsaro a kan iyakar Atmeh wanda ke karkashin ikon 'yan tawaye a lardin Idlib.

'Yan tawayen da aka kashe na samun goyon bayan kasar Turkiyya ne, kuma suna yakar kungiyar IS, wacce ke ikirarin kafa daular Musulunci.

Ba a dai tabbatar da ko dan kunar bakin wake ne ya kai harin ko kuma na'urar tada bomb ce ta haddasa ba.

Wani kamfanin dillancin labarai, wanda ke da alaka da kungiyar IS, ya ce wata motar kunar bakin wake ce ta kai hari kan jerin gwanon motocin 'yan tawayen.

Sai dai wata kungiyar 'yan adawa, ta rawaito cewar an dasa wata akwati dauke da bama-bamai a wurin da aka kai harin.

A cikin watan Agusta ne dai aka kai wani harin kunar bakin waken a kan iyakar Atmeh, wanda IS din ta dauki alhakin kai wa.